Hafinity Market
Hausa
English

Dokoki da Ka'idoji

Barka da amfani da Hafinity Market . Wadannan dokoki ne da suka shafi kowane mai amfani (Buyer, Vendor, ko Guest) a wannan dandalin.

1. Rajista da Bayanan Masu Amfani

Ta hanyar yin rajista, ka amince ka samar da sahihan bayanai kamar Cikakken Suna, Garin da kake (Location), da Lambar Waya. Kai ne ke da alhakin kare sirrin password dinka.

2. Ka'idojin Masu Sayarwa (Vendors)

  • Dole ne dukkan kayan da aka dora su zama masu inganci kuma na gaskiya.
  • Admin yana da ikon duba (Approve) ko goge (Delete) kowane kaya idan ya saba wa ka'ida.
  • Za a cire kaso na commission (kamar yadda aka saita a Settings) daga duk cinikin da aka kammala.

3. Wallet da Cire Kudi

Ana adana kudin mai sayarwa a cikin **Wallet**. Ana iya neman cire kudi (Withdrawal Request) bayan mai saya ya karbi kayansa kuma oda ta zama 'Delivered'.

4. Tsaro da Tuntuba

Hafinity Market tana kare hakkin mai saya da mai sayarwa. Idan aka samu matsala, za a iya amfani da sashen **Contact Admin** domin sasantawa.